1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

191109 EU-Sondergipfel Bilanz

November 20, 2009

Shugabannin Ƙasashen Duniya sunyi maraba da sabbin shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai da aka naɗa

https://p.dw.com/p/KbxV
Herman Van Rompuy da Catherine AshtonHoto: AP

A jiya ne ƙungiyar tarrayar turai ta zaɓi sabon shugaban ƙasa na ƙungiyar na farko, muƙamin da aka baiwa Piraiminstan ƙasar Beljium, an kuma zaɓi wanda zai shugabacin harkokin siyasa na ƙetare a ƙungiyar, inda 'yar ƙasar Birtaniya wacce ke riƙe da muƙamin komishiniyar kasuwanci na ƙungiyar EU a halin yanzu. Usman Shehu Usman na ɗauke da ƙarin haske.

Da fari dai mutane da dama sun ɗauka wannan zaɓen zai jawo tada jijiyar wuya, to amma akasin haka aka samu. Tun a wajejen yammacin jiya shugaban ƙasar Siwidin, ƙasar dake riƙe da shugabancin ƙungiyar EU a halin yanzu ya nuna alamun inda za ta kaya, wato dai mai riƙe da muƙamin Piraiministan ƙasar Beljium shi zai ɗare kan wannan muƙamin a karo na farko, inda kuma ƙololuwar siysayar turai a ƙitare, za ta je ga hannun 'yar ƙasar Birtaniya Cathrin Ashton, wanda kafin yanzu itace komishinyar kasuwancin na ƙungiyar ta EU. Shugaban ƙasar ta Siwidin Fredrik Reinfeldt yace.

"Abin da muke biɗa shine mutanen da za su kawo cigaba. su iya kawo mana haɗin kai, waɗanda za su kasance muryoyi da fisakar turai a dukkan faɗin duniya. To kuma ina ganin mun cimma wannan burin"

Deutschland Angela Merkel Bundestag Regierungserklärung
Angela MerkelHoto: AP

Wannan dai yana nufin samun mutanen da suka ɗora a kujerar shugabancin majalisar da shugabannin ƙasashen tarayyar turai ke haɗuwa. Shi ma sabon shugaban ƙasa na tarrayar turai Hemman Van Rompuy ya yi ƙarin haske bayan tabbatar da shi a wannan muƙamin.

"Ra'ayin hukumar ya danne nawa ra'ayin, wato nawa tunanin dai bashi da tasiri. Aikina shine abin da hukumar ta amince a akai"

Ita kuwa matar da aka miƙawa babban muƙamin a wannan ƙungiyar na kula da siyasar ƙitare, ta karɓi muƙamin da jawabin kawar da sukar da ake yi mata na cewa ba ta da ƙwarewar riƙe wannan muƙamin.

"Ina ganin ƙwarewa ta za ta nuna da kanta, shin ina da wani koɗoyi a'a bani da shi, inaso a riƙa jina a'a. Ku yanke hukunci a kai na bisa abinda nayi, kuma nayi imanin za ku gamsu, kuyi alfahari da ni".

Der schwedische Ministerpräsidenten Fredrik Reinfeldt (Ausschnitt)
Fredrik ReinfeldtHoto: picture-alliance/dpa

Ƙasar Jamus tana daga ƙasashen da suka taka mahimmiyar rawa wajen samun kaiwa ga wannan zaɓen, wanda zai ƙara tabbatar da haɗin kai a tarrayar turai, kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel take cewa.

"Wannan ya nuna a zahirin haɗin kai a tsarin turai, abin da kuma ya nuna cewa ra'ayoyi daban-daban, idan suka haɗu to daga ƙarshe ana iya ɗaukar matsayi guda, kuma waɗannan ra'ayoyi sune suka haɗu har aka samu ƙarfin yin hakan"

Sabon shugaban ya kawar da rahotonnin da kafafen yaɗa labarai ke yaya tawa, na cewa ba shi da ƙwarewar aiki wanda har zai iya riƙe muƙami mai girma kamar wannan,inda yace muna shirya mu sauke nauyin da aka ɗora mana.

Mai riƙe da muƙamin shugaban humar zartarwata ƙungiyar tarayyar turai, Manuel Barosso ya yi maraba da wannan zaɓen, inda ya ce ba'ayi zaɓen tumun dare ba. domin wanda aka zaɓan ya na da ƙwarewa ta shugabanci.

Shi ma shugaban ƙasar Amirka Barack Obama, ya aika da saƙon taya murna ga sabon shugan ƙasa na ƙungiyar tarrayar turai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu