Sabbin sauye-sauye a Jam´iyyar ANC | Labarai | DW | 18.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin sauye-sauye a Jam´iyyar ANC

A wani lokaci a nan gaba wakilan Jam´iyyar ANC a Afrika ta Kudu za su fara kaɗa kuri´a, don zaɓen sabon shugaban Jam´iyyar. Zaɓen da za a gudanar a arewacin birnin Polokwane na samun halarcin wakilai kusan 400. Ana dai wannan takara ne, a tsakanin shugaba Thabo Mbeki da kuma tsohon mataimakinsa Mr Jacob Zuma. Takarar shugabannin, a yanzu haka ta haifar da darewar Jam´iyyar ta ANC izuwa gida biyu. A shekara ta 2005 ne Mr Mbeki ya tsige Jacob Zuma daga muƙaminsa, bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa. Rahotanni sun ce duk da waɗannan zarge-zarge da alama Zuma ka iya lashe wannan zaɓe na yau. Matuƙar kuwa ya samu wannan nasara, to babu makawa Mr Zuma ka iya zamowa shugaban Afrika ta kudu a shekara ta 2009. Kundin tsarin mulƙin ƙasar dai ya hanawa Mr Mbeki yin tazarce a karo na uku, bayan ƙarewar wa´adinsa na biyu a shekara ta 2009.