1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

D Westerwelle Afghanistan

July 9, 2010

Ministan harkokin wajen Jamus ya ba da sanarwar gwamnati akan sabbin manufofinta dangane da Afghanistan

https://p.dw.com/p/OFUi
Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle na ba da sanarwar gwamnati kan sabbin manufofinta dangane da AfghanistanHoto: AP

Kwanaki goma kafin a gabatar da taron ƙasa-da-ƙasa akan ƙasar Afghanistan a birnin Kabul, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ba da sanarwa akan manufofin gwamnati dangane da ƙasar ta Afghanistan a majalisar dokoki ta Bundestag. Sai dai kuma 'yan hamayya sun yi sukan cewar ministan harkokin wajen bai taɓo ainihin matsalar dake akwai ba.

Bisa ta bakin ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, gwamnati ta canza salon kamun ludayinta a manufofinta dangane da ƙasar Afghanistan tun bayan taron ƙasar da aka gudanar a birnin London, inda take ba da fifiko ga matakai na gaggawa wajen horar da sojoji da 'yan sandan Afghanistan.

"An cimma dukkan waɗannan manufofin a cikin watanni shidan da suka wuce. Wannan taƙaitaccen sakamako ne mai muhimmanci ko da yake ba a cimma biyan dukkan buƙatu ba."

A cikin sanarwarsa game da manufofin gwamnati dangane da Afghanistan Westerwelle ya ce Jamus gudanar da gagarumin aiki a Afghanistan kuma zata ci gaba da yin hakan duk da shirin gwamnati na tsuke bakin aljihu..

"Ba zamu yi wata tsumulmular kuɗi a ayyukan da muke gabatarwa a Afghanistan ba, saboda fatan cimma nasarar da muke yi da kuma cikakkiyar masaniyar da muke da ita game da alhakin dake kanmu. Jamus na kan alƙawarinta."

Dukkan jam'iyyun dake da hannu a gwamnatin haɗin guiwa a fadar mulki ta Berlin sun yaba da manufofin Afghanistan dangane da 'yan watannin da suka wuce. To sai dai kuma duk da wannan nasara, lamarin da walakin. Domin kuwa sau tari akan rasa makomar wasu kuɗaɗe na taimako ko kuma ma a zuba su a akwati a fitar da su zuwa ƙetare, a yayinda cin hanci ke daɗa bunƙasa kuma har yau Afghanistan ba ta da kyakkyawan tsaro. Sojojin Jamus guda bakwai aka kashe tun abin da ya kama daga farkon wannan shekara. Bisa ga ra'ayin 'yan hamayya hakan na yin nuni ne da cewar babu wani ci gaba na a zo a gani da ake samu a Afghanistan bisa saɓanin iƙirarin da gwamnati ke yi. Gernot Erler jami'in jam'iyyar Social-Democrats yayi nuni da cewar sabuwar manufar dangane da Afganistan bata tsinana kome ba.

"Duk da cewar sojojin ƙasa-da-ƙasa kimanin dubu 150 aka tura zuwa Afghanistan, amma har yau ana ci gaba da fuskantar hare-hare na sare ka-noƙe. Kuma watan yunin da ya gabata ya zama mummunan wata na zub da jini da asarar rayuka a tarihin aikin sojan zaman lafiya a Afghanistan inda aka kashe sojoji 102."

Su kuma 'yan The Greens sun zargi Westerwelle ne da kwane-kwane a maimakon taɓo ainihin matsalar da sojojin NATO da kuma sojan tsaro na Jamus ke fama da ita. Kazalika suka ce ministan bai ce uffan ba a game da wahalar da ake fama da ita wajen sasantawa tsakanin su kansu rukunonin da ba sa ga maciji da juna a ƙasar Afghanistan. An saurara daga bakin Frthjof Schmidt daga jam'iyyar ta The Greens yana mai faɗi cewar:

"Mai gima ministan harkokin waje, duk da cewar mun fahimci mawuyacin halin da ma'aikatarka ke ciki, amma yau a gaskiya ka ba ni kunya, saboda na so na ji kalamai masu ma'ana daga gare-ka."

A nasa ɓangaren dai Westerwelle nuni yayi da cewar sauran batutuwan da ba a taɓo su ba za a tattauna su a zauren taron ƙasa-da-ƙasa kan Afghanistan da aka shirya gabatarwa a Kabul ranar 20 ga wata. Kuma kasancewar wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan taro a Kabul, hakan na mai yin nuni ne da irin ci gaban da ake samu bisa manufa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu