Sabbin hare-haren ta′addancin a yankin arewacin Rasha. | Siyasa | DW | 31.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabbin hare-haren ta'addancin a yankin arewacin Rasha.

Halin da ake ciki a yankunan arewacin ƙasar Rasha bayan sabbin hare-hare a ranar laraba

default

 Wani harin ƙunar baƙin -  waken da aka ƙaddamar  yau laraba a yankin Caucasus dake arewacin ƙasar Rasha, ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 12, galibinsu kuma 'yan Sanda ne.

Hare-haren ƙunar baƙin wake guda biyun da suka tashi a yankin Caucasus na arewacin ƙasar Rasha dai, sun yi sanadiyyar mutuwar Jami'an 'yan Sanda 9, da wani babban mai gabatar da ƙara na gwamnati guda ɗaya, a yayin da wasu mutane 23 kuma suka sami rauni, inda hukumomi suka garzaya da su zuwa asibiti.

Waɗannan hare haren sun zo ne yini biyu kachal bayan a safiyar ranar litinin data gabata,  an ƙaddamar da wasu guda biyu a layin dogon ƙarƙashin ƙasa na Moscow, babban birnin Rasha waɗanda kuma hukumomin na Rasha suka danganta da mayaƙan sa kai na yankin Caucasus.

Da farko dai bam ya tashi ne a wata mota, bayan da matuƙin ya ƙi tsayawa a lokacin da jami'an 'yan Sanda suka bashi umarnin ya dakata, kana kimanin mintuna ashirin bayan haka kuma, sai wani ɗan ƙunar bakin wake sanye da kakin 'yan Sanda ya tayar da wani bam ɗin a dai dai lokacin da yake tsakiyar gungun 'yan Sandar dake ƙoƙarin tantance bam na farko.

Dukkan hare haren biyu, sun afku ne a garin Kizlyar dake yankin Dagestan - kusa da kan iyakar Chechny, yankin da ke yawaita samun tashe tashen hankula tun sa'adda mahukunta a birnin Moscow suka ƙaddamar da yaƙi na biyu akan 'yan awaren Chechny.

Tuni dai, ministan kula da harkokin cikin gida a Rasha Rashid Nurgaliyev ya buƙaci 'yan ƙasar dasu kula sosai ga waɗanda ya kira masu aikata laifi akan bil'adama:

Russland Dagestan Anschlag in Kisljar

" Da alama ayyukan masu tada tarzoma a 'yan kwanakinnan na nuni da cewar, a shirye suke su lalata komai. Saboda haka, akwai buƙatar ɗaukacin al'umma su kula sosai."

Ministan na magana ne bayan da hare haren baya bayannan suka yi sanadiyyar rugujewar wasu sassa na gine-ginen wata makaranta - ko da shike hukumomin Rasha suka ce, babu ɗalibai a lokacin da lamarin ya afku.

Frime ministan Rasha Vladmir Putin, ya bayyana cewar, yana da amannar hare haren wannan larabar, suna da alaƙa da na ranar litinin, wanda ake zargin wasu Mata biyu daga yankin Caucasus, mai rinjayen musulmai da kaiwa.

Mr Putin, ya ce, cikin ɗan ƙaramin lokaci gwamnati zata gano gungun masu yin wannan aika-aikar:

"  Mun san cewar, suna ɓoye ne a karƙashin ƙasa, kuma alhakin jami'an tsaro ne kaiwa garesu. Sannu a hankali, sai sun damƙesu kuma a -wulaƙance."

Putin auf dem Parteitag von Einiges Russland

Priminista Vladimir Putin

Ko da shike hukumomin Rasha sun bayar da umarnin tura ƙarin jami'an tsaro a yankin Caucasus, mazarta da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a sun yi gargaɗin cewar, duk wani yunƙurin daƙile masu tada ƙayar baya a yankin zai ƙara ruruta wutar fitinar ce kawai, maimakon daidaita lamura.

A jawabin da ya yiwa kwamitin tsaron ƙasar kuwa, Shugaban Rasha Dmitry Medvedev, ya bayyana cewar, tuni ya sanya hannu akan dokar tsaurara lamuran tsaro a ɓangaren sufuri, inda ya ƙara jaddada buƙatar hukumomi su shawo kan matsalolin talauci da kuma cin hancin daya zama ruwan dare a Caucasus - a matsayin hanyar kawo ƙarshen tada tarzoma a yankin.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh Edita: Zainab Mohammed