Sabbin hare-hare a Syria
February 19, 2018Talla
Rahotannin dake fitowa daga Syria, na cewa wasu jiragen yakin gwamnatin kasar sun yi luguden wuta a gabashin Ghouta, bayan samun bayanan yiwuwar fuskantar artabu daga mayakan tawaye da ke a yankin. Gabashin na Ghouta wanda yanki ne na karshe da ya saura a hannun 'yan tawaye a kewayen birnin Damascus, na fuskantar fushin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, bayan aikewa da wasu zaratan dakaru 'yan hadarin safe maganin uba mai tsanani.
Ko a farkon wannan watan ma dai, sai da mayakan gwamnati suka dauki kwanaki biyar cur suna ruwan boma-bomai, inda shaidu suka ce akalla fararen hula 250 sun salwanta, wasu daruruwan kuma suka ji jiki.