1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hare hare a Iraqi

Wani karamin jirgin yaki mallakar kasar Amurka, ya kai harin bama bamai izuwa matsugunan yan fadan sari ka noke dana kwanton bauna a garin Kirkuk, dake arewacin kasar Iraqi.

Bayanai dai sun shaidar da cewa a lokacin harin, an samu galabar kashe yan fadan sari ka noken a kalla guda 10.

A cewar jami´an sojin Amurka dake gudanar da aikin kiyaye zaman a Iraqi, wannan harin ya biyo bayan gano wasu mutane uku ne suna dasa bama bamai , a kusa da wata babbar hanya dake wajejen garin na Kirkuk.

Bayan dai wannan hari, jamian sojin na Amurka sun kuma karbe wasu makamai da alburusai da kuma sanadaran kera bama bamai na cikin gida , daga hannun wasu mutane dake yankin da wannan abu ya faru.