1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya

An kori dukkan hafsoshin tsaron Najeriya, a ƙasa da watanni biyar kafin zaɓukan shugaban ƙasa da na gwamnoni da 'yan majalisun ƙasar.

default

Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kori hafsoshin tsaron ƙasar inda yanɗa wasu sabbi nan take. Daga cikin waɗanda aka kora sun haɗa da janaral Abdurrahman Dambazau, inda aka maye gurbinsa da Onyeabor Azubike Ihejirike, sai kuma shugaban rundunar sojin ruwa Ishaya Ibrahim wanda aka maye gurbinsa da Rear Admiral Ola Sa'ad Ibrahim, shi kuwa Air Vice Marshal Mohammed Dikko Umar yanzu shine aka naɗa babban hafsan sojin sama. Yayinda aka ƙarawa tsohon babban hafsan sojin sama Air vice Mashal Oluseyi Petirin girma, a yanzu shine babban hafsan tsaronƙaras. Shi ma dai sipeto janar na 'yan sandan Najeriya Ogbonna Onovo korar ta shafe shi, inda yanzu aka naɗa Alhaji Hafiz Ringim a matsayin sabon sipeto janar na 'yan sandan ƙasar. Sai kuma darkatan 'yan sandan ciki wato SSS, inda yanzu aka naɗa Ita Ekpeyong a matsayin sabon daraktan hukumar bayan da aka kori Afakriya Gadzama. Sanarwar fadar shugaban ƙasar dai tace naɗe naɗen sun fara aiki nan take, ko da yake a bisa dokar tarrayar Najeriya sai majalisa dokokin ƙasar ta amince da naɗin kafin ya fara aiki.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu