Sabani tsakanin AU da UN kan Darfur | Labarai | DW | 22.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabani tsakanin AU da UN kan Darfur

An samu sabanin raayi tsakanin mdd da kungiyar tarayyar afrika Au adangane kasashen dakarun kiyaye zaman lafiya dubu 26, da ake shirin turawa zuwa lardin Darfur.Sun dai ta hakikance cewar,akwai dakarun kasashen Afrika da zasu isa turawa,amma shugabannin mdd sun bayyana cewar ,dakarun Afrikan baszasuyi wani tasiri ba,idan baa gaurayasu da na wasu kasashen da ba na Afrika.Bugu da kari Wani mai fada aji daga shugabannin kungiyoyin yan tawayen Darfur din,ya jaddada cewar,sabbin dakarun su fito daga wata nahiyar amma ba Afrika ba,sabanin haka zasu kauracewa taron sasantawa da zaa gudanar a kasar Libya a karshen watan gobe.Majiyar Amurka kuwa ya nunar dacewa,duk wani shugaban adawa da bai halarci taron na Libya ba,zaa kakaba masa takunkumi.