Sabani kan shirin Mr Bush a tsakanin yan majalisar dattijai | Labarai | DW | 18.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabani kan shirin Mr Bush a tsakanin yan majalisar dattijai

Majalisar dattijan Amurka ta kada kuri´ar kin amincewa da tattauna wani kuduri da Mr Bush ya gabatar, wanda zai yi watsi da shawarar karin soji a Iraqi.

A karo na 2 a cikin mako daya, jam´iyyar Democrat ta gaza samun rinjaye na tattauna wannan batu.

Yan jam´iyyar ta Democrat dai na adawa ne da shirin na Mr Bush, da cewa babu abin da zai haifar illa kara dagula al´amurra a iraqi.

Tuni dai yan jam´iyyar Republicans suka tabbatar da cewa ,gaza karin soji a Iraqi, ka iya haifar da karin fitintinun yan fadan sari ka noke da kuma na kwanton bauna.