1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani kan kasafin kudin 2018 a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
November 28, 2017

Sabanin ra'ayi ya dabaibaye kasafin kudin Janhuriyar Nijar na 2018. Gamayyar kungiyoyin farar hula na kasar sun nuna rashin amincewa da shi, bayan da 'yan majalisar dokoki suka kada kuri'ar amincewa.

https://p.dw.com/p/2oOWg
Mahamadou Issoufou Premierminister von Niger
Hoto: picture alliance/S. Minkoff

Hadin gwiwar kungiyoyin farar hular a Jamhuriyar Nijar masu kyama ga kasafin kudin 2018 ne suka bayyana aniyarsu na kalubalantar sabon kasafin kudin da majalisar dokokin kasar ta rattabawa hannu.

Kungiyoyin dai sun ce haramtacce ne saboda saba ka'idojin doka ta kundin tsarin mulki. Duk da shawarwarin da suka shigar a gaban majalisa don kawo sauki ga wasu tanade tanaden da sabon kasafin ya kunsa da suka ce bai dace da al'umma ba, majalisar ta jefa kuri'ar na'am da sabon kasafin.

A cewar gamayyar kungiyoyin farar hular Nijar dai, abun mamaki ne yadda majalisar a makon da ya gabata ta amince da kasafin da gagarumin rinjaye, duk da cewar mafi yawa daga cikin al'ummar kasar sun nuna adawa da ita.

Dangane da haka ne suka nunar da manufarsu na mikewa tsaye domin kalubalantar wannan mataki na yunkurin aiwatar da kasafin na shekara ta 2018 duk da adawa da suka yi.

Sai dai a yayin da ake samun ra'ayi zazzafa wasu 'yan farar hula sun ce kasafin ya yi daidai. Kasancewar ya tanadi sabbin batutuwa da suka zo a lokacin da ake bukatarsu.