Sabani akan Schröder | Siyasa | DW | 03.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabani akan Schröder

Ana sabani a game da karbar shugabancin kwamitin zartaswa na kamfanin Gasprom na Rasha da Schröder yayi

Gerhard Schröder

Gerhard Schröder

Bisa ga ra’ayin sakatare-janar na jam’iyyar CDU Ronald Pofalla dai, babu wani aibu a game da tsaya wa kamfanin makamashin Rasha na Gaprom da gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens tayi domin ba wa kamfanin rancen kudi. Pofalla ya ce:

Matsalar dake akwai shi ne a game da yanayin ba da wannan lamuni. Domin kuwa a halin yanzu dukkan tsofon shugaban gwamnatin da ministocinsa na kudi da na harkokin waje na ikirarin cewar bas u da wata masaniya game da lamarin.

Gerhard Schröder dai ya sha nanata cewar ba ya da wata masaniya a game da shawarar da aka tsayar a wancan lokaci. Wannan furucin nasa tamkar martani ne yake mayarwa akan zargin da ake yi na cewar tun a matsayinsa na shugaban gwamnati ne Schröder ya share hanyar darewa kann wannan sabon mukamin da ya samu a kamfanin na Gasprom. A makon da ya gabata ne tsofon shugaban gwamnatin na Jamus ya kama aikinsa a matsayin shugaban kwamitin zartaswa na kamfanin dake tafiyar da ayyukan sabbin bututan gas a yankin east sea. A yayinda ‚yan the Greens ke kira ga Schröder da yayi watsi da wannan mukami, ita jam’iyyar SPD kariya take ba shi. An ji daga Hubertus Heil, sakatare-janar na jam’iyyar yana mai fadin cewar:

Kafa wadannan bututan gas da zasu ratsa tekun east sea na da muhimmanci game da maslahar Jamus. A saboda haka ya zama wajibi mu wayar da wakilan sauran jam’iyyun a game da cewar bai kamata a saboda dalilai na manufofin jam’iyya su yi watsi da muhimmancin wannan shiri ga maslahar kasa ba. Wannan maganar musamman ta shafi jam’iyyar FDP.

Bisa ga ra’ayin Hubertus Heil, jam’iyyar FDP dai kokari take ta shafa wa tsofuwar gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens kashin kaza. Bisa ga ra’ayin jam’iyyar, duk da cewar kamfanin na Gasprom yayi fatali da tayin lamuni da tsofuwar gwamnatin tayi masa, amma duk da haka wannan manufar wata mummunar tabargaza ce kuma a saboda haka take shawarar gabatar da rokon kafa wani kwamitin bincike na majalisar dokoki da zai bi bahasin lamarin. A dai halin da ake ciki yanzun da wuya jam’iyyar ta cimma biyan bukata. To sai dai kuma da yake ana neman karin haske, a jibi laraba idan Allah Ya kai mu kwamitin kasafin kudin kasa na majalisar dokoki zai bi tushen matsalar da ake ci gaba da sabani kanta.