1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani akan kisan gillar da aka yi wa jami'an tsaron Jamus guda biyu a Iraki

April 14, 2004

Kisan gillar da aka yi wa wasu jami'an tsaron Jamus su biyu dake kan hanyarsu daga Amman ta kasar Jordan zuwa Bagadaza a Iraki, shi ne ya dabaibaye siyasar cikin gidan kasar yanzu haka

https://p.dw.com/p/Bvki
Jami'an tsaron Jamus guda biyu da aka rasa makomarsu a Iraki
Jami'an tsaron Jamus guda biyu da aka rasa makomarsu a IrakiHoto: dpa

Bisa ga ra’ayin gwamnati a fadar mulki ta Berlin, jami’an tsaron su biyu da tsautsayin kisan gillar ya rutsa da su akan hanyarsu daga Amman zuwa Bagadaza ba su yi ragon azanci na tafiya ta kasa ba. Ana amfani da wannan hanya tsakanin Iraki da Jordan domin jigilar kayayyaki da ma’aikatan ofisoshin jakadancin Jamus dake kasashen biyu. Har dai ya zuwa ranar laraba ta makon jiya, inda ga alamu jami’an tsaron suka yi asarar rayukansu, wannan hanyar bata da wani hadari. A lokacin da yake bayani kakakin ma’aikatar cikin gida Rainer Lingenthal cewa yayi:

Karin bayani da nike so in yi muku a nan shi ne kasancewar an sha amfani da wannan hanyar sau da dama a zamanin baya ba tare da an fuskanci wani hadari ba. Ba shakka a game da cewar tilas ne mutum ya rika taka tsantsan wajen kai da komonsa dangane da halin da ake ciki a Iraki a yanzun kuma a saboda haka ba za a iya batu a game da wasu hanyoyi marasa hadari a kasar ba. Kazalika ba zata yiwu a ce an yi ragon azanci wajen zabar wannan hanya da aka sha amfani da ita a zamanin baya ba tare da wani hadari ba.

‚Yan hamayya dai sun kwatanta wannan tafiya ta mota tamkar wata "Kundumbala zuwa lahira". A ganinsu da abu mafi alheri shi ne jami’an diplomasiyyar da na tsaro na Jamus su zarce zuwa Bagadaza ta jirgin sama. A mayar da martani ga wannan zargi fadar mulki ta Berlin ta ce, jami’an tsaron daga rundunar tsaron iyaka ta GSG 9 ta Jamus, ba zasu iya amfani da jirgin saman fasinja a cikin damararsu ta makamai ba. Kazalika ba zasu iya amfani da jirgin saman sojan Amurka ba, saboda a kebe jiragen ne domin amfanin sojojin taron dangi a kasar Iraki kawai. Kawo yanzun dai babu wani cikakken bayanin da ake da shi dalla-dalla a game da tsautsayin da ya rutsa da jami’an tsaron na Jamus su biyu. Rahotanni dai sun nuna cewar ayarinsu da ya kunshi motoci shida ya rabu da babbar hanyar a kusa da Falluja saboda sojojin Amurka sun toshe hanyar. Bayan haka, ga alamu, aka bude wuta kan motocin. Kuma ko da yake gwamnati ba ta tabbatar da mutuwar jami’an da aka dora musu alhakin tsaron ofishin jakadancin Jamus a Bagadaza ba, amma akalla tana binciken lamarin. Wadanda suka shaida abin da ya faru da idanuwansu har yau suna cikin hali na kaduwa ta yadda ba za a iya fuskantarsu da tambayoyi ba. Da zarar an samu sakamakon binciken, ministan cikin gida Otto Schily, a shirye yake ya amsa tambayoyin kwamitin majalisar dokoki ta Bundestag, wanda alhakin lamarin ya rataya wuyansa. Babu dai wani shirin da aka tanadar domin rufe ofishin jakadancin Jamus ko na sauran kasashen Kungiyar Tarayyar Turai a birnin Bagadaza. Abin da gwamnati ke fata shi ne sake mika wa alö’umar Iraki ikon cin gashin kansu, kamar yadda aka shirya, a karshen watan yuni mai zuwa ta yadda MDD zata samu damar taka rawar gani wajen sake gina kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita.