Sabani a game da sabon shugaban hukumar zartarwa ta KTT | Siyasa | DW | 28.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabani a game da sabon shugaban hukumar zartarwa ta KTT

Gwamnatin Jamus ta bayyana damuwa da takaicinta a game da sabanin dake akwai tsakanin hukumarzartarwa ta KTT da majalisar Turai dangane da sabon shugaban hukumar da tawagarsa

Sabon shugaban hukumar zartarwa ta KTT Jose Manuel Barroso

Sabon shugaban hukumar zartarwa ta KTT Jose Manuel Barroso

Ba tare da wata rufa-rufa ba shugaban gwamnatin Jamus Gerhard schröder ya bayyana damuwarsa tare da takaicin takaddamar da ake fama da ita tsakanin hukumar Kungiyar Tarayyar Turai da majalisar Turai a lokacin wani taron da yayi da manema labarai a fadar mulki ta Berlin, yana mai bayyana fatan ganin an shawo kan lamarin nan ba da dadewa ba. Schröder ya kara da cewar:

A wannan halin da muke ciki yanzun ba zamu saduda da wata baraka tsakanin kafofin KTT ba. Domin hakan na ma’anar mummunan koma baya. Muna bukatar wata kakkarfar hukuma dake da ikon zartaswa, musamman a yanzun, inda kungiyar ke da kasashe 25 karkashin tutarta. Babban abin da ake bukata shi ne hadin kai tsakanin kafofin amma ba sabani bisa wasu dalilai na dabam ba.

To sai dai kuma ita jam’iyyar The Greens, mai hadin guiwa da SPD tayi marhabin da shawarar da Jose Manuel Barroso ya tsayar na dakatar da kuri’ar raba gardamar a game da tawagar wakilan hukumarsa. A lokacin da suke bayani dukkan shuagabannin jam’iyyar The Greens guda biyu Claudia Roth da Reinhard Bütikhofer sun bayyana cewar wannan shawarar wata manufa ce dake kara tabbatar da tsarin demokradiyya a nahiyar Turai. An ji irin wannan bayanin daga wakilan ‚yan Christian Union, inda kakakinsu a manufofin Turai Peter Hintze ya ce shugaban hukumar zartaswar ta KTT dake jiran gado ya nuna halin sanin ya kamata ya kuma hana kungiyar fadawa cikin wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi. To sai dai kuma ba dukkan ‚yan Christian Union ne ke da wannan ra’ayi ba, inda wasu ke nuni da cewar a yanzu haka dai hukumar ba ta da shugaba, kuma tsofon shugabanta Romano Prodi ba zai iya ba ta wani sabon jini ba.