Saban rikici ya ɓarke a Lal Massadjid | Labarai | DW | 27.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saban rikici ya ɓarke a Lal Massadjid

Masu tsautsauran ra´ayin addinin Islama na ƙasar Pakistan sun sake mamaye Lal Massajid dake birnin Islamabad.

Idan dai ba a manta ba,yau da sati 2 da su gabata, sojojin gwamnati su ka murƙushe tarzomar da yan takifen massalacin su ka tada, bayan kwanaki da dama a na gumurzu.

Yan takifen sun kori saban limamin massalacin da a aka naɗa, a lokacin da ya zo jagorantar sallar juma´a.

Sannan sun fara maida jan pentin massalacin da gwamnati ta goge.

Sun yi ta rera kalamai masu nuna adawa ga shugaban ƙasar Pakistan Pervez Musharaf.

A halin da ke ciki jamai´an tasaro, sun janye daga harabar wannan massalaci.

Kakakin opishin ministan cikin gida, ya ce gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace, a lokacin da ya dace, domin maido doka da oda, a cikin Lal Massajid.