Saban rikici ya ɓarke a gabacin Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo | Siyasa | DW | 21.11.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Saban rikici ya ɓarke a gabacin Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo

An yi fito na fito, tsakanin dakarun gwamnati da ´yan tawaye a yankin Kivu na Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo.

default

kura ta turnuke a yankin Kivu

A na ci gabada ɓarin wuta a kudancin Jamhuriya Demokradiyar Kongo, tsakanin sojojin gwamnatin da dakarun Janar Lauran Nkunda.

Rahotani daga Rutshuru da ke yankin Kivu a gabacin Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo, sun tabbatar da cewa, anyi ɓarin wuta mai tsanani, da sanhin sahiyar yau, tsakanin sojojin Gwamnati ,da dakarun Janar Lauran Nkunda.

Wata majiyar gwamnati tace, a ƙalla sojojin 20 daga ɓangaren ´yan tawaye suka rasa rayuka a cikin wannan gumurzu, sannan da dama suka ji mummunan raunuka.

Saidai ´yan tawayen sun musanta wannan adadi.

Ya zuwa yanzu, babu wata majiya mai zaman kanta da ta bada gaskiyar labarin.

A cewar Kantoman yankin Rutshuru, Antoine Mushima, sojojin ukku kawai suka ji raunuka daga ɓangaren dakarun gwamnati, wanda kuma a halin yanzu ke ci gaba da samun magani a babbar asibitin sojoji ta Rutshuru.

Kantoman yayi kira ga jama´a ta kwantar da hankali, saidai da alamun wannan kira bai samu karɓuwa ba.

A halin da ake ciki, dubunan mutane ke ci gaba da ƙauracewa gidajensu

Tun shekara guda da ta wuce gabacin Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo ke fuskantar tashe-tashen hankulla masu tsanani, wanda ya zuwa yanzu, suka saka mutane kussan miliyan ɗaya a cikin halin gudun hijira.

Duk da cewar dakaru dubu ɗaya na Janar Nkunda sunyi saranda yaci gaba da jan daga a arewacin Kivu, inda yace sai ya ga abinda ya turewa buzu naɗi.

Shugaban Jamhuriya Demokradiyar Kongo, Joseph Kabila ya ba rundunar „FARC“ umurnin ta kwance ɗamara yaƙin ´yan tawayen ta ko wane hali.

Don cimma wannan mataki, Gwamnati ta jibge dakaru kussan dubu 20 a arewancin Kivu.

Wata sanarwar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a yammacin yau, ta nunar da cewar ƙura ta lafa a yankin Kivu, kuma rundunar shiga tsakani ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara sintiri, domin kwantar da hankulan jama´a.

A cewar Sylvie van den Wildenberg, kakakin rundunar MONUC ta Majalisar Ɗinkin Duniya, a wajejen ƙarfe ɗaya, ´yan tawayen su ka amince su ja da baya.

To saidai a zahiri, har yanzu jama´ar Kudancin Kivu na cikin wani yanayi na ruɗani.

 • Kwanan wata 21.11.2007
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CQ7H
 • Kwanan wata 21.11.2007
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CQ7H