1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saban rikici ya ɓarke a DRC

February 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuSV

Shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, William Swing, ya bayyana matuƙar damuwa, a game da hauhawar tashe-tashen hankulla, da kuma taka haƙƙoƙin bani adama a wannan ƙasa.

Idan dai ba manta ba, ranar juma´a da ta wuce, wani saban rikici ya ɓarke a yammacin ƙasar, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kussan 80.

Tashin hankalin ya biwo bayan bayyana sakamakon zaɓen gwamna a yankin, wanda mai goyan bayan shugaban Joseph kabila, ya lashe.

Swing, ya zargi sojoji da yan sanda ƙasar, da aikata kissan kan uwa mai uwa da wabi, inda kuma ba ayi hattara ba, wannan al´amari kan iya maida hannun agogo baya, a game da yar ƙwarya-ƙwaya lafawar ƙura da a aka samu , bayan zaɓen shugaban ƙasa.