Saban Praministan Thailand ya girka gwamnati | Labarai | DW | 09.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saban Praministan Thailand ya girka gwamnati

Saban Praminstan ƙasar Thailand Jannar Surayud Chulanont, ya bayyana sunayen ministocin gwamnatin da ya girka, bayan juyin mulkin ranar 19 ga watan Satumber na wannan shekara, wanda ya hamɓara da Takhsin Shinawatra.

Daga cikin jerin ministoci 26 da wannan gwamnati ta ƙunsa 2 ne kawai sojoji.

Kakakin gwamnatin ya sanar cewa, mai martaba Sarkin Tahiland, yayi ammana da wannan sabuwar gwamnati, wace zata fara dukufa aiki tun daga yau litinin.

Masu nazarin harakokin siyasa a ƙasar, sun ce Gwamnatin ta ƙunshi massana zalla, misali an naɗa shugaban babbar bankin ƙasar a matsayin ministan kuɗi, sannan wani goggage ta fannin harakokin diplomatia, ya hau muƙamin minsitan harakokin waje.

Wannansabuwar gwamnati da ta kunshi mata guda 2 kawai na da wa´adin shekara kamin farfado da demokradiya a ƙasar Thailand.