Sa hannu kan kudurin zaman lafiya a Kwalombiya | Labarai | DW | 23.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sa hannu kan kudurin zaman lafiya a Kwalombiya

Gwamnati da 'yan tayawen FARC duk sun amince kan sabon kudurin kawo karshen yakin basasa da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 220,000 kana miliyoyi suka rasa mahallinsu.

Yarjejeniyar farko dai an yi watsi da ita lokacin zaben raba gardama a watan Oktoba, inda masu zabe suka nuna cewa an yi fifiko ga 'yan tawaye cikin kudurin. Sai dai kudurin da aka yi wa dan kwaskwarima, wanda za a sanya wa hannu a ranar Alhamis a Bogotá, babban birnin kasar, kusan kananan gyare-gyare ne kawai aka yi masa. An kuma bayyana cewa a wannan karon ba a bukatar 'yan kasa su yi kuri'a, illa kawai za a mika wa majalisar dokoki ta yanke hukunci a kai. Akalla mutane dubu 220 suka mutu a yakin basasan kasar ta Kwalombiya.