1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saƙon Paparoma na Kirsimeti

Paparoma Benedict na 16 ya yi kira ga mabiya addinin kirista da su keɓe lokaci daga cikin aiyukansu domin bautawa ubangijinsu da kuma kula da gajiyyayu.Paparoma ya faɗi haka ne wajen jawabinsa na bukin kirsimeti da ake gudanarwa yau a koina cikin duniya.Yace mutane da dama sun yi watsi da addininsu basu da lokaci na tunawa da wanda ya halicce su,da makwabta da kuma gajiyayyu.Cikin jawabin nasa Paparoma ya kuma yi kira ga kare muhalli don ci gaban alumma.