1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saɓanin ra´ayi tsakanin Bush da Rice a game da Irak

November 15, 2006
https://p.dw.com/p/Buc2

Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice,ta yi watsi da shawarwrin Tony Blair, da komitin James Becker, a game da hanyoyin hita daga ƙangin ƙasar Irak.

Rice ta ƙi amincewa, da ra´ayi da Praminista Blair ya bayyana, na cewa, rashin cimma nasara warware rikicin gabas ta tsakiya, ya ta´allaka ga yaƙin Iraki.

Matsaloli ne guda 2, da bai kamata a gama ba, inji Condoleesa Rice.

A ɗaya wajen, ta yi watsi da shawara tsoma bakin Iran da Syria a yunƙurin warware wannan rikici.

Tace Amurika ba zata taba amincewa ba, da tantanwa da maƙiyan ta a game da harakokin siyasa da na diplomatia da su ka shafi wasu ƙasashe daban.

Gwamnatin Georges Bush, ta shiga wani hali, na tsaka mai yuwa, tun bayan kayin da ta sha, a zaɓen yan majalisar da aka gudanar a Amurika ranar 7 ga watan da mu ke ciki.