Ryan ya kare dokar shugaba Trump | Labarai | DW | 31.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ryan ya kare dokar shugaba Trump

Kakakin majalisar dokokin Amirka Paul Ryan ya kare dokar shugaban kasar da ta haramtawa kasashen musulmi shiga Amurka da ya dauki hankalin duniya a halin yanzu, yana mai nadamar rudanin da batun ya haifar.

 

 Ryan dai ya ce hakki ne kan shugaban Amurka ya tabbatar da tsaron kasar, amma a daya hannun ya ji takaicin yadda matakin ya shafi baki masu tasiri ga kasar, musamman masu aikin fassara da matakin ya shafa.

Kakakin majalisar ta Amurka ya kuma ce tilas a dakata a kuma waiwayi harkokin baki da na 'yan gudun hijiran kasar ne saboda matakan tsaro na kasa.

Shuagabn Amurka Donald Trump dai, ya haramtawa baki daga kasashen Siriya da Yemen da Iran da Iraki da Somalia da

Libya da kuma Sudan ne na watanni uku, yayin da 'yan gudun hijira kuwa watanni hudu.

Daga yanzu kuwa babu batun zaman 'yan hijiran Siriya a kasar, a wani mataki na illa masha Allahu.