1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rwanda tayi watsi da batun kama shugaba Kagame

November 21, 2006
https://p.dw.com/p/Buaz

Kasar Rwanda tayi watsi da kira da wani alkalin kasar Faransa yayi mata na ta kama shugaba Paul Kagame da laifin da da aka zarginsa da shi cikin kisan tsohon shugaban kasar.

A jiya litinin ne dai alkali Jean Louis Bruguiere yace ya kamata a gurfanar da Kagame gaban kotun kasa da kasa mai sauraron laifukan yaki a Tanzania bisa zargin hannu cikin kisan tsohon shugaba Juvenal Habriyamana.

An kuma rigaya an bada warantin tsare wasu jamian gwamnatin Kagame su 9,cikinsu har da babban hafsan sojin kasar.

Tun farko Kagame yayi ta karyata cewa yana da hannu cikin wannan kisa wanda ya haddasa kisan kiyashi a akasar,wanda yayi sanadiyar mutuwar yan kabilar tutsi akalla 800,000 da kuma yan hutu masu sassaucin raayi.