1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rwanda ta janye jakadanta daga Faransa

Kasar Rwanda ta janye jakadanta daga Faransa sannan ta yi barazanar katse huldodin diplomasiya da Faransa. Hakan dai ya zo ne bayan da wani alkali a Faransa ya ba da takardar kame jami´an Rwanda su 9 bisa zarginsu da hannu a kisan kare dangi da aka yi a Rwandar a shekara ta 1994. dukkan mutanen su 9 na kurkusa ne da shugaba Paul Kagame, wanda alkalin ya ce ya zarga da hannu dumu-dumu wajen harbo jirgin saman da tsohon shugaban kasar Juvenal Habyarimana ke ciki. Mutuwar shugaban ne kuwa ta janyo kisan kare dangin da aka yiwa dubun dubatan ´yan Tutsi da kuma ´yan Hutu masu sassaucin ra´ayi. Shugaba Kagame ya yi watsi da zargin da alkali Jean-Luis Bruguiere yayi da cewa da akwai wata manufa ta siyasa a ciki. Dangantaka tsaakanin Faransa da Rwanda ta yi tsami, inda shugaba Kagame ke zargin Faransar da rashin yin wani abin kirki na hana aukuwar kisan kiyashin.