1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rwanda da laifukan yaƙi na Kwango

Rwanda ta ce za ta ƙauracewa shirin wanzar da zaman lafiya a Darfur idan Majalisar Ɗinkin Duniya idan ta zargeta da aikata laifukan yaƙi a Kwango Demokaraɗiya.

default

Ƙasar Rwanda ta yi barazanar janye dakarunta daga Sudan da zarar Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargeta da aikata kisan ƙare dagi a Jamhuriyar Demokaraɗiyar Kwango. Kakakin sojojin ƙasar ta Rwanda wato Leftenan Kanal Jill Rutaremara ya ce ƙasarsa ba za ta yi wata-wata ba wajen ficewa daga aikin wanzar da zaman lafiya a Darfur da ya ƙunshi sojojinta dubu uku da 300 ba, idan aka dangantata da mai kashe-kashen bai gaira.

Wannan barazanar ta zo ne a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke shirin wallafa rahoto da zai zayyana irin rawar da sojojin ƙasashe da dama ciki har da na Rwanda suka taka a ta'asar da aka aikata a yaƙe-yaƙe biyu da Jamhuriyar Demokarɗiyar ƙwango ta fiskanta. A 'yan kwanaki da suka gabata ma, sai da gwamantin Rwanda ta yi barazanar taƙaita hulɗa da MDD, matiƙar aka sanyata a jerin ƙasashen da suka aikata laifukan yaƙi a kwango a shekarun 1996 da kuma 1998.

Ita dai ƙasar ta Rwanda ta danganta wannan rahoton da MDD za ta wallafa da wani yunƙuri da ba zai haifar da ɗa mai ido ba a yankin tsakiyar Afirka.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala