1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Russia ta zargi Amirka da katsalandan a harkokin cikin gidanta

Ibrahim SaniNovember 27, 2007
https://p.dw.com/p/CTZL

Shugaba Bush na Amirka ya buƙaci Gwamnatin Russia da ta sako ´Yan adawa da masu kare hakkin bil´adama da ta cafke a makon daya gabata. Ci gaba da tsare mutanen a cewar Mr Bush, abune daka iya kawo hautsini na siyasa a ƙasar. Shugaban na Amirka ya kuma tabbatar da cewa matakin na Russia, abune na take hakkin bil´adama. Rahotanni sun shaidar da cewa an cafke ´Yan adawan ne, a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe a biranen Mosco da St. Petersburg, a makon daya gabata ne. Ɗaukar matakin yazo ne a dai- dai lokacin da ƙasar ke shirye- shiryen gudanar da zaɓen ´Yan majalisun dokokin ƙasar ne. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito shugaba Vladimir Putin na Russia na zargin Amirka da tsoma baki, a cikin harkokin siyasar ƙasar. Yin hakan a cewar Mr Putin abune da ka iya kawo cikas, a game da zaɓen da ake shirin yi a ranar 2 ga watan Disambar wannan shekara.