Rushewan bene a lagos ya kashe mutane da dama | Labarai | DW | 19.07.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rushewan bene a lagos ya kashe mutane da dama

A kalla mutane 4 ne suka rasa rayukansu ,kana wasu masu yawa suka makale ,alokacinda wani ginin bene mai hawa hudu ya rushe a birnin Lagos,dake zama cibiyar hada hadan kasuwancin Nigeria.Tun jiya da safe ne wannan makeken gidan sama dake dauke da dakunan kwana da shaguna a unguwar Ebute Metta dake lagos din.Acikin daren jiya nedai aka zakulo gawawwakin mutane 4.Wadanda suka ganewa idanunsu yadda wannan gini ya rushe,sun bayana cewa wadanda suka mutun ,mazauna gidan ne da suka dawo daga aiki.Kakakin yansanda a lagos Bode Ojajuni,,yace an kaddamar da bincike a dangane da musabbabin rushewan wannan gidan bene,wanda ke zama na baya bayan nan a wannan birni,mai mafi yawan jamaa a nahiyar Afrika.
 • Kwanan wata 19.07.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6A
 • Kwanan wata 19.07.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6A