1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rushe hukumar kare hakkin yan Adam ta MDD

March 28, 2006

A bayan shekaru sittin, an rushe hukumar kare hakkin yan Adam ta majalisar dinkin duniya

https://p.dw.com/p/BvTh
Zauren shawara na hukumar a Geneva
Zauren shawara na hukumar a GenevaHoto: AP

Hukumar kare hakkin yan Adam ta majalisar dinkin duniyajiya Litinin tayi zaman taron ta na karshe, wanda kuma bayan sa ne akia rushe hukumar baki dayan ta, bayan aikin da tayi na fiye da shekaru sittin. Nan gaba kadan ake sa ran za’a kirkiro wata sabuwar majalisar shawara ta kare hakkin yan Adam, wadda zata gurbin hukumar da aka rushe a jiya.

Ana dai iya cewar karshen hukumar ta kare hakkin yan Adam ta majalisar dinkin duniya yazo ne ba tare da hakan ya dauki hankalin kowa ba. A zauren taron an gudanar da wasu yan jawabai na yabon aiyukan wannan hukuma, to amma bayan yan awoyi kalilan, kowa ya watse. Duk da haka, karshen hukumar ta majalisar dinikin duniya ya zaman abin tunani, game da makomar batun kare hakkin yan Adam baki daya. Ana iya tambayar: shin sabani a hukumar, game da batun kare hakkin yan Adam har sun kai munin da ya zama tilas ne bayan shekaru sittin na aiyukan ta, amma cikin dare daya, ba zato, ba tsammani a rushe ta?

Babu shakka abubuwan da suka faru a zaurukan hukumar kare hakkin yan Adam ta majalisar dinkin duniya a Geneva tun daga yan shekarun baya abubuwa ne na bakin ciki ne. Hukumar ta dade bata cikin haiyacin ta, ta dade bata iya tabuka wani abin kirki a game da aiyukan da aka danka mata alhakin tafiyarwa. A maimakon ta maida hankalin ta game da makomar al’ummar da suka kasance cikin mummunan hali na rayuwa da azabtarwa da wadanda basu da yancin siyasa, sai tafi maida hankali ga al’amura na siyasa. Sau da dama hukumar takan nuna hali na fuskoki biyu. Duk kasar da ta kasance mai karfi ko kuma take da kasashe magoya bayan ta masu angizo, kakar ta yanke saka, bata da abin da zata ji tsoron sa a wannan hukuma. A karshe dai hukumar sai ta dare gida biyu: A hannu guda, akwai kasashe masu karfi wadanda su kansu suke daukar matakai na keta hakkin yan Adam, amma suka mamaye aiyukan ta. Irin wadannan kasashe sun rika kare junan su a hukumar. A daya hanun kuma, akwai kasashe marasa gata, wadanda duk laifin duniyar nan na keta hakkin yan Adam aka dora a kansu. Amerika, wadda ta taba kasancewa jagora kann batun kare hakkiny an Adam, tayi asarar mutunci da darajar ta mai yawa saboda matakan da take dauka kann hanyar yaki da aiyukan tarzoma. Kungiyar hadin kann Turai bata da karfin da ake bukata ta wannan fuska, yayin da kasashen cikin ta suka kasa samun wata manufa ta bai-daya game da batun na kare hakin yan Adam.

Ana dai iya ganin dacewar matakin rushe hukumar ta kare hakkin yan Adam da kuma maye gurbin ta da wata sabuwar majalisar shawara, to sai dai yadda aka tafiyar da wnanan al’amari ne bai dace ba. Cikin dare daya aka rushe tsohuwar hukumar aka kuma yanke kudirin kirkiro wadda zata gaje ta. Duk da haka idan ma akwai wani abin dake da kyau a game da wnanan mataki, shine yadda taron babbar mashawartar majalisar dinkin duniya zata zabi wakilai a sabuwar hukumar da za’a kafa. Hakan zai baiwa kasashe da ake zargin su da laifukan keta hakkin yan Adam matukar wahala a kokarin su na samun kujeru a sabuwar majalisar. Masu goyon baya da masu adawa da matakan kare hakkiny an Adam sun daidaita a kann cewar duk kasar dake bukatar a zabe ta a sabuwar majalisar wajibi ne ta sami kashi hamsin cikin dari na yawan wakilan tarion na majalisar dinkin duniya, maimakon kashi biyu cikin kashi ukku na kuri’un wakilai a da. Saboda haka a sabuwar majalisar kamar dai a wadda aka rushe, za’a sami wakilcin kasashen da ake zargin su da keta hakkin yan Adam. Hakan nan kuma, wakilcin sabuwar majalisar za’a tsara shi ne yadda zai dace da nahiyoyin duniya. Sai dai duk da wadannan gyare-gyare, muddin sabuwar majalisar ta kare hakkin yan Adam za’a kafa tana bukatar tafiyar da aiyukan ta yadda ya dace, tilas ta kasance da karfin siyasa, ta kuma rika gudanar da aiyukan ta ba sani, ba saboda. Ko da shike ganin yadda aka rushe tsohuwar hukumar da kuma kirkiro wata a yanzu, yana da wuya a gane irin darasin da aka koya daga kura-kuran da aka yi a can baya.