Rundunonin tsaro a Israila suna atisaye mafi girma a kasar | Labarai | DW | 20.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunonin tsaro a Israila suna atisaye mafi girma a kasar

Rundunonin tsaro a Israila sun fara wani atisaye mafi girma da suka taba yi a tarihin kasar suna masu sake duba darussan tsaro da kariya da suka koya wajen yakinsu da Hezbollah.

Atisayen na kwanaki biyu ana yi ne a bangarori daban daban na Israila,inda suke yin gwaji na hare haren muggan makamai da makami masu guba.

Kimanin yan sanda 5,000 da sojoji 6,000 da kuma jamian kashe gobara suke gudanar da wannan atisaye .