Rundunara sojin Jamus ta dakatar da sojojinta da sukayi laifi a Afghanistan | Labarai | DW | 27.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunara sojin Jamus ta dakatar da sojojinta da sukayi laifi a Afghanistan

Rundunar sojin kasar Jamus ta dakatar da sojoji 2 sakamakon batun nan na hotunan sojoji da aka nuna suna dauke kwarangwal din kann mutum a kasar Afghanistan.

Wajen wani taro da manema labarai a birnin Berlin ,ministna harkokin tsaro na Jamus Franu Josef Jung yace ana nan ana kuma binciken wasu sojojin 2 biyowa bayan nuna wasu hotunan kuma da gidan TV na Jamus RTL yayi a jiya alhamis,wandanada aka ce an dauka a 2004.

Jung yace babban jamiin horaswa na rundunar sojin Jamus zai tafi zuwa Afghanistan don sake duba aiyukan sojin na Jamus a can.

Reinhold Robbe shine wakilin rundunar sojin Jamus a majalisar dokokin kasar.

Cikin wata hira da jaridar Jamus daily Bild,wacce ta fara buga hotunan,daya daga cikin sojojin yace,wannan abu ya faru na 2003 kusa da birnin Kabul,sakamakon tashin hankali da su sojojin suke ciki.