Rundunar sojin haɗin gwiwa a Dafur | Labarai | DW | 08.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar sojin haɗin gwiwa a Dafur

Sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya yi kira ga gwamnatin Sudan ta hanzarta shirin kafa rundunar haɗin gwiwa na Afrika da Majalisar ɗinkin duniya waɗanda za su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Dafur. Sai dai kuma a hannu guda jamián gwamnatin sudan a birnin Khartoum sun ɗora laifi a kan ƙasashe masu bada gudunmawa wajen kawo jinkiri ga shirin tura sojojin. A wani jawabi da ya gabatar wa kwamitin sulhun majalisar ɗinkin duniya, Ban Ki Moon yace halin da ake ciki a Dafur yana kan wani siratsi na tsaka mai wuya. Yce taron sulhun da aka gudanar a ƙasar Libya a watan da ya gabata ya bada da kyayawar dama da ya kamata dukkan ɓangarorin sun yi amfani da ita domin tura dakarun kiyaye zaman lafiyar cikin gaggawa. Sakataren Majalisar ɗinkin duniya yace jinkirta tura sojojin ka iya haifar da rashin kwanciyar hankali da kassara alámura a lardin na Dafur. Amurka da sauran ƙasashen Turai na zargin shugaban ƙasar Sudan Hassan Omar al Bashir da haifar da tsaiko wajen fara tura sojin kiyaye zaman lafiyar.