Rundunar sojin Amurka tayi cajin wasu sojojinta da kisan fararen hula a Iraqi | Labarai | DW | 22.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar sojin Amurka tayi cajin wasu sojojinta da kisan fararen hula a Iraqi

Rundunar sojin Amurka tayi cajin wasu sojojinta su 8 bisa hannu da suke da shi kisan a kisan wasu farar hula na Iraqi su 24 a garin Haditha.

Anyi cajin hudu daga cikin sojojin da laifin kashe wadannan mutane saura hudun kuma an kama sune da laifin kin bada rahoto ko kuma gudanar da bincike game da kisan na yan Iraqin.

Kanar Stewart Navarre ya sanarda manema labarai game da cajin da akayiwa sojojin

Sojojin dai zasu iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai.

A watan nuwamba na 2005 ne sojojin na Amurka suka kashe farar hula 24 a garin Haditha a matsayin ramuwar gaiya na mutuwar wani sojin Amurka cikin wani harin bam na gefen hanya.