Rundunar sojin Amurka ta shirya kai wani babban dauki a Bagadaza | Labarai | DW | 05.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar sojin Amurka ta shirya kai wani babban dauki a Bagadaza

Rundunar sojin Amurka tace tana shirin kai wani babban dauki da baa taba ganin irinsa a Birnin Bagadaza tare da nufin tabbatar da tsaro a babban birnin kasar ta Iraki.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Amurka a Iraki Kanar Doug Heckman ya fadawa manema labarai cewa,a yau litinin ne zaa shirya rundunoni da zasu kai wannan dauki.

Dakarun na Amurka cikin wannan dauki zasu ratsa ne dukkan tituna da gidajen birnin Bagadaza daya bayan daya inda zasu karbe makamai tare da cafke yan bindiga dake birnin.

A karshen mako ne mutane fiye da 130 suka rasa rayukansu cikin hare haren bam mafiya muni tun bayanda Amurka ta mamaye Iraki.