Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da hari a kudancin Somalia | Labarai | DW | 09.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da hari a kudancin Somalia

Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da hari ta jiragen saman yaki kan wadanda ta kira yan kungiyar Alqaeda da suka kai harin bam kan ofisoshin jakadancin Amurkan a kasashen Kenya da Tanzania a 1998.

Kafofin yada labarau na Amurka sun bada rahotonnnin cewa jirgin yakin Amurka kirarar AC 130 ya kai hari daga Djibouti zuwa kudancin Somalia bayan jamian leken asirin Amurka sun gano wadanda ake nema.

Rahotannin sunce daya daga cikin wadanda ake nema da laifin kai harin,wani shugaban al Qaeda a gabashin Afrika.