Rundunar shiga tsakani a Libanon | Labarai | DW | 22.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar shiga tsakani a Libanon

Kurt Beck, shugaban jam'iyyar SPD.

Kurt Beck, shugaban jam'iyyar SPD.

Majalisar Dinkin Dunia, ta matsa ƙaimi wajen tantanna batun samar da rundunar shiga tsakani, zuwa kudancin Libanon, bayan tsagaita wutar da a ka cimma a rikicin da ya hada Isra´ila da dakarun Hizbullahi.

Kussan kwanaki 10 bayan dakatar da yakin ya zuwa Majalisar ta kassa hada yawan dakarun da ake buƙatar kaiwa a yankin.

A jawabin da yayi jiya shugaban kasar Amurika Georges Bush ya bukaci gagaguta tuwa wanna runduna.

Ƙasar Italia, ta bayana aniyar karɓar jagorancin wannan runduna, da ta zata ƙunshi, a ƙalla dakaru dubu 15.

Saidai kamar sauran ƙasashen Turai, Romano Prodi, ya buƙaci Majalisar Dinkin Dunia,ta haƙiƙance yaunin da ya rayata akan rundunra.

EU ta gayyaci sakatare jannar Koffi Annan zuwa Bruxelles domin tananta wannan batu.

To saidai, ta fannin zaman lahia har yanzu yan gudun hijira da su ka koma gidajen su, na zama cikin halin ruɗani, ta la´akari da, hare -hare jefi jefi, da Isra´ila ke ci gaba da kaiwa, duk kuwa da tsagaita wutar.

Kazalika, a ɓangaren Palestinu rundunar Isra´ila, ta kai karin samame, wanda a sahiyar yau, su ka yi sanadiyar mutuwar mutane 3 a zirin Gaza.