Rundunar NATO ta kai hari ga yankunan yant aliban a Afghanistan | Labarai | DW | 06.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar NATO ta kai hari ga yankunan yant aliban a Afghanistan

Dakarun ƙungiyar tsaro ta NATO a ƙasar Afghanistan sun bayana ƙaddamar da wani gagaramin shiri na yaki da yan Taliban a yankin Helmand da ke kudancin ƙasar.

A jimilce, NATO ta baza sojoji kussan dubu 6, wanda a ka ɗorawa yaunin ƙwato wannan yanki daga hannun mayaƙan taliban.

Wannan shine hari mafi girma, da sojojin ƙasa da ƙasa su ka ƙaddamar, tun lokacin da su ka shiga Afghanistan.

Ya zuwa yanzu Rundunar ISAF, a Afghanistan ta bayyana mutuwar sojan ta 1 a cikin arangamar da ta hada ta yau da dakarun Taliban.

Saidai al´ummomin wannan ƙasa, a sahiyar yau talata , sun shirya wata babbar zanga-zanga, domin yin Allah wadai, da sojojin taron dangin, mussaman na Amurika.

Masu zanag-zangar, sun yi ta rera kalamomi, inda su ka yi ta ƙurma zagi, ga shugaba Georges Bush na Amurika, da yan amshin shatan sa.

Wannan zanga-zanaga ta biwo bayan kissan gillar da sojojin Amurika, su ka yi wa wasu mutane 10, yan ƙasar Afghanistan.