Rundunar NATO a Afghanistan ta bukaci ƙarin sojoji | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar NATO a Afghanistan ta bukaci ƙarin sojoji

Babban komadan na rundunar tsaro ta NATO, Jannar James Jones, ya bayyana matuƙar mamaki, a game da turjiyar, da yan taliban ke ci gaba da yi, a ƙasar Afghanistan.

A dangane da haka, ya yi kira ga ƙasashe membobin ƙungiyar da su gaggauta kara yawan dakarun a wannan yankin inda ake cigaba da bata kashi tsakanin sojojin ƙasa da ƙasa, da mayaƙan taliban.

Gobe da jibi, idan Allah kai mu, komitin zartaswa na rundunar NATO, zai zaman taro, a birnin Warso, inda za su tantana a kan sabin hanyoyin ɓullo ma, turjiyar mayaƙan taliban.

Shima shugaban rundunar Isaf a kasar Afghanistan, Jaap de Hoop Scheffer, ya nuna goyan baya ga kara yawan sojojin a kasar domin fuskantar yan taliban:

Turjewar yan taliban ta zarta fiye da kima, yadda mu ka zata a farkon shiga Afghanistan.

Saboda haka, ƙasashe membobin NATO su ka alkawarta ƙara yawan dakaru.

Mu na kyautata zaton, ko wace ƙasa za ta tunani cikin gaggawa, ta kuma biya bukatar ƙarin sojojin, da Jannar James Jones da ni kai na, mu ka tambaya.