Rundunar MDD ta gama aiki a kasar Haiti | Labarai | DW | 06.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar MDD ta gama aiki a kasar Haiti

Bayan shekaru 13 ta na ayyukan samar da tsaro, rundunar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Haiti ta Minustah ta kawo karshen aikin duk da cewa akwai rikici na siyasa a kasar.

Haiti UN Mission Blauhelme UN Mission (picture-alliance/AP Photo/D.N.Chery)

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a kasar Haiti sun gama aiki

Shugabar rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Haiti Sandra Honore ta ce har yanzu akwai sauran ayyuka da dama da ta kamata a yi a kasar ta Haiti kafin ta kai matsayin da kowane dan kasar ke fatan gani.

A shekara ta 2004 ne dai aka girka rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Haiti bayan ficewar shugaban kasar Jean-Bertrand Aristide domin kwantar da tashe-tashen hankulan da aka fuskanta musamman a Port-au-Prince babban birnin kasar, sai dai kuma rundunar ba ta samu yarda daga 'yan kasar ba, musamman magoya bayan tsohon shugaban kasar.