Rundunar Isra´ila ta kai samame a zirin Gaza. | Labarai | DW | 29.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar Isra´ila ta kai samame a zirin Gaza.

A halin da ake ciki, cen yankin na gabas ta tsakiya, rundunar tsaron Isra´ila, na ci gaba da ɓarin wuta a zirin Gaza, a yunƙurin ta na ƙwato, Caporal Gilad Shalit, da wasu yan takife ,su ka ɗauke ranar lahadin da ta wuce.

A cikin wannan halin kuma, rundunar tsaron ta gano gawar wani bayahude, a yamma ga kogin Jordan, da wata ƙungiyar Palestinawa ta ɗauki alhakin yi wa yankan rago.

A daren jiya, sojojin Isra´ila,sun capke da dama daga shugabanin ƙungiyar Hamas, da su ka haɗa da ministoci da, yan majalisun dokoki 68, da kuma ƙarin mutane masu yawa.

Sojojin Isra´ila sun watso ta sararin samaniya, takardun da ke kira, ga al ummomin yankin, da su ƙauracewa wuraren da su ke kai samamen, domin sun yi alƙawarin belin Caporal Shalit, ta ko wane hali.

Saidai ministan tsaron Isra´ila, Amir Peretz, ya ce basu da wani saban buri na mamaye zirin Gaza.

Dakarun Isra´ila, za su hito da zaran sun cimma burin da ya kai su.