1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar ISAF ta sake halaka fararen hula a Afghanistan

September 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuAm
Akalla ´yan tawaye 50 aka kashe a wani kazamin fada da aka fafata tsakanin dakarun kawance da mayakan ´yan Taliban a Afghanistan. Wata sanarwa da rundunar sojin kasa da kasa a Afghanistan ISAF ta bayar ta ce an gwabza fadan ne a lardin Uruzgan dake kudancin kasar sai kuma wani gumurzu da aka yi a lardin Badghis dake arewa maso yammacin Afghanistan inda aka kashe wani soja dan kasar NL. Rundunar ta ISAF ta tabbatar da mutuwar fararen hula da dama a wani hari da jiragen saman yakin ta suka kai a lardin Helmand a ranar laraba da ta wuce. Wani labarin da ya zo mana yanzu yanzu na cewa an kashe wani soja dan kasar Faransa sannan fararen hula da dama sun mutu ko kuma sun jikata a wani harin kunar bakin wake da aka kan kan wani ayarin sojojin Faransa a birnin Kabul dazu-dazun nan.