1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar da kungyiar EU ta girke a Kongo ta kammala aikinta

November 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuZd
Bayan wa´adi na wata 4 rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr ta kammala aikinta a kasar JDK. Yanzu haka dai wa´adin aikin rundunar EUFOR karkashin jagorancin rundunar ta Bundeswehr, wadda kungiyar EU ta girke a Kongon ya kare. Ma´aikatar tsaron Jamus dake birnin Berlin ta yaba da nasarar wannan aikin da sojojin kasar suka yi a Kongo. Ta ce rundunar ta EUFOR ta taka muhimmiyar rawa a zaben ´yan majalisar dokoki da na shugaban kasa da aka gudanar a Kongon.