1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rundunar Bundeswehr na bikin cika shekaru 50 da kafuwa.

A cikin wannan shekarar ne, rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr ke bikin cika shekaru 50 da kafuwarta. Kazalika kuma, a lokaci daya ne za a yi bikin cika shekaru 15 da hade rundunonin soji na Jamus ta Gabas da ta Yamma, karkashin laimar rundunar ta Bundewehr. A ran 7 ga watan Yunin shekara ta 1955 ne aka kafa ma’aikatar tsaro ta tarayyar Jamus, wato Jamus Ta Yamma, a wannan lokacin. A cikin watan Nuwamban wannan shekarar ta 1955 ne kuma, farkon rukuni na rundunar sojin ta Bundeswehr ya fara aikinsa. Ko me rundunar ta cim ma a tsawon wannan lokacin ?

Wasu sojojin Bundeswehr suna ba da taimamon agaji a Banda Aceh na kasar Indonesiya, bayan girgizar kasar da aka yi a can.

Wasu sojojin Bundeswehr suna ba da taimamon agaji a Banda Aceh na kasar Indonesiya, bayan girgizar kasar da aka yi a can.

A lokacin da aka tsai da shawarar kafa rundunar soji ta kasar Jamus a cikin shekarar 1955, sai da aka yi ta muhawara mai tsanani a majalisu da kuma a bainar jama’a. Saboda a wannan lokacin, ana dab ke nan da cika shekaru 10 da kawo karshen yakin duniya na biyu, wanda ya janyo wa Jamus din ragargajewar kasarta gaba daya, bayan ta sha mummunan kaye a hannun dakarun kawance karkashin jagorancin Amirka. Al’umman Jamus a wannan lokacin dai suna nuna kiyayyarsu ne ga sake kafa wata rundunar soji kuma, wadda a nasu ganin za ta iya tsunduma su cikin wani bala’in kuma. Kazalika kuma, jam’iyyar adawa ta SPD a wannan lokacin, ta yi gargadin cewa kafa rundunar, da shigarta cikin kungiyar NATO za ta dagula duk yunkurin da ake yi ne na cim ma hadewar kasar, wadda sakamakon yakin duniyan na biyu, ta rabu a sassa biyu, wato Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma.

Sai dai, a daura da fargabar da aka yi da farko, rundunar ba ta kasance wata sabuwar kafa ta yada mulkin danniya kamar a lokacin `yan Nazi ba. Wato an sami wata sabuwar runduna ne, wadda ke nuna cikakkiyar biyayya ga gwamnatin dimukradiyya, duk da cewa wasu daga cikin farkon manyan hafsoshinta, sun yi aiki karkashin gwamnatin Nazi ta Hitler.

Tun kafuwarta har zuwa shekarar 1989, za a iya cewa rundunar ta sami nasarar tabbatad da tsaro a Jamus ta Yamma, da samad da zaman lafiya a Turai da kuma kawo karshen yakin cacar baka, ba tare da harba bindiga ko sau daya ba. Wata nasarar kuma, wadda ba a cika ambatonta ba, ita ce maido da rundunar sojin Jamus ta Gabas, karkashin rundunar ta Bundeswehr, bayan hadewan kasashen Jamus din guda biyu, ba tare da wata matsala ba.

Tun daga nan ne dai kuma, ake ta yi wa tsarin rundunar kwaskwarima, don ta iya huskantar sabbin kalubalen da ke kunno kai a cikin gida da kuma a fagen siyasar kasa da kasa. Ba za a iya dai mantawa da tura rukunan soji na rundunar ta Bundeswehr zuwa yankunan da ake rikici a duniya a karo na farko ba. Girke dakarun da aka yi a Bosniya, da Kosovo, da Afghanistan da kuma a kahon Afirka na bayyana irin sabbin kalubale da kuma nauyin da suka rataya a wuyar rundunar, a gamayyar kasa da kasa.

A halin yanzu dai, kusan dakarun rundunar Bundeswehr dubu 35 ne ke girke a ketare. A nan ne ministan tsaro Peter Struck ya yi gangamin cewa, rundunar ta kai matukar da ba za ta iya ba da gudummuwar soji ga wani dauki kuma a kasashen ketare ba, idan dai ana son ta iya cim ma burinta na kare Jamus. Su dai dakarun na Jamus, ba dakaru ne na mamaye ba, a daura da dakarun wasu kasashen kamar na Amirka a Iraqi. Aikinsu ne kare zaman lafiya da taimakawa wajen sake gina yankunan da yaki ya ragargaza, kamar jihar Kundus ta Afghanistan.

Yanzu dai tambayar da ake yi a nan cikin gida, game da makomar rundunar ita ce, wai shin za ta kasance rundunar bauta wa kasa ne bisa tsarin da aka kafa ta a shekaru 50 da suka wuce, ko kuwa za a yi mata kwaskwarima ne ta zamo wata tsangya ta sana’ar aikin soji ? Jam’iyyun siyasa dai kamarsu Greens, da FDP da wani bangare ma na jam’iyyar gwamnati ta SPD, na neman a soke tsarinta na kasancewa rundunar bauta wa kasa, a mai da ita kafar sana’a ta aikin soji.

To amma masharhanta da dama na ganin cewa, ba wannan tambayar ce ta fi muhimmanci ba. Muhimmin batun da ke da alamar tambaya a kansa shi ne na ko Jamus a shirye take ta tura dakarunta zuwa fagen yaki a ketare, kamar Amirka ko Birtaniya ?

Wannan dai wata sabuwar muhawara ce, da za a dade ana ta tattaunawa a kanta. A cikin wata fira da ya yi da mujallar nan ta FOCUS ta nan Jamus, ministan tsaro na tarayya, Peter Struck, ya ce idan dai Jamus za ta tura dakarunta zuwa yankunan da ake yaki, to ya kamata kuma ta kwana da shirin cewa, babu shakka, wasu daga cikin sojojin za su rasa rayukansu a bakin daga. Tuni dai, wasu `yan majalisa sun fara bayyana adawarsu ga wannan sabon salon.

Kawo yanzu dai, ka’idar da majalisar dokoki ke aiki da ita wajen tura dakarun Jamus zuwa ketare ita ce, sai an tabbatar da cewa dakarun ba za su yaki wani bangare a ketaren ba kafin a tura su can. Za su yi harbi ne kawai wajen kare kansu idan aka kai musu farmaki, amma ba su shiga gwabza yaki da `yan kasar da aka tura su gudanad da aikin kare zaman lafiya ba. Amma furucin da ministan tsaro Peter Struck ya yi, babu shakka zai janyo rudami da kuma wata muhawar mai tsanani tsakanin wakilan jam’iyyun siyasa a majalisar dokokin tarayya ta Bundestag.

 • Kwanan wata 07.06.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbT
 • Kwanan wata 07.06.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbT