1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

170608 AFRICOM Afrika USA

Duckstein, Stefanie (DW Afrika)June 17, 2008

A nan Jamus ana ƙara sukar rundunar soji da Amirka za ta kafa ga Africa.

https://p.dw.com/p/EL3T
Kwamandan Africom Vice Admiral Robert MoellerHoto: Vince Crawley, U.S. Africa Command

Birnin Stuttgart na nan Jamus ne hedkwatar sabuwar rundunar Amirka dangane da Afrika wato Africom. A farkon wannan shekara an dakatar da shirin neman wuri mafi dacewa don kafa reshenta a Afirka saboda adawa da shugabannin wannan nahiya suka nuna. To sai dai a nan Jamus ma ana ƙara sukar wannan runduna ta Africom.


Willy Wimmer masanin harkokin ƙetare na jam´iyar CDU ya na nuna damuwa dangane da kafa wannan rundunar sojin Amirka ga nahiyar Afrika wato Africom.


Wimmer ya ce "Dukkanmu mun san cewa Amirka ta girke sojoji a ko-ina cikin duniya sannan yanzu tana karkata akalarta ga nahiyar Afirka. Ba aikin taimako ko na wata ƙungiyar agazawa ´yan gudun hijira zata kafa ba, kamata ya yi mu san cewa burinta shi ne kare buƙatunta na soji."


Yanzu haka dai hedkwatar rundunar na da sojojin Amirka 550 sannan a cikin watan Oktoba yawansu zai kai sojoji dubu 1 da 300 ciki ma´aikatan tsaro masu zaman kansu. Wimmer na mai ra´ayin cewa rundunar wata barazana ce Jamus saboda haka dole ne ta ɓace daga yankin ƙasar Jamus. Wimmer ya ba da misali da abin nan da ya shafi babban kamfanin tsaro da aikin soji mai zaman kansa na Amirka wato Blackwater a Iraqi, inda ma´aikatansa suka kashe fararen hula 17 a Bagadaza a shekara ta 2007. To sai dai kakakin kamfanin Vince Crawley ya yi watsi da wannan suka yana mai cewa ai Afirka ba Iraqi ba ce.


Crawley ya ce "Ina sane da fargabar da ake nunawa. Yana da muhimmanci a fahimci dangantakar wannan lamari da aikinmu a Iraqi da Afghanistan. Halin da ake ciki a Afirka ya bambamta domin a can rigakafin aukuwar yaƙe-yaƙe za mu yi. Za mu yi ƙoƙarin samar da yanayin inda ƙasashen Afirka za su iya samun ci-gaba da wadata ga al´ummominsu."


Crawley ya ƙara da cewa yaƙe-yaƙen a Iraqi da Afghanistan sun ɗauki hankalin sojojin Amirka saboda haka aka dogara ga wani kamfanin tsaro mai zaman kansa.


Masu sukar lamirin rundunar ta Africom na ƙorafin cewa rundunar kaɗai ba zata iya tinkarar wata barazana ta ´yan ta´adda ko masu fataucin miyagun ƙwayoyi da makamai ba.


Nancy Walker ta shafe shekaru 10 ta na jagoran shirin ma´aikatar tsaron Amirka dangane da Afirka, ta a nuna shakku da aikin raya ƙasa da aka ce rundunar Africom zata yi, tana mai cewa ai Amirka na da hukuma ta musamman ta ba da taimakon raya ƙasashe masu tasowa.


Nancy Walker ta ce "Shin gwamnatin Amirka ta na son ta nuna kenan zata ƙara taka rawa a aikin raya ƙasashen Afirka ko sha´awar samun cikakken haɗin kai da Afirka saboda haka ta ke son ta danƙawa dakaru ko kamfani mai zaman kansa wannan aiki? Abin dai da walakin, wai shin me ya sa mutane a cikin kayan sarki za su karɓi ragamar aikin raya ƙasa?"


Masu sukar wannan shiri na ciki da wajen Afirka musamman ƙungiyar tarayyar Afirka da ƙasashe kamar Afirka ta Kudu da tarayyar Nijeriya na nuna fargaba game da mayar da manufofin Amirka kan Afirka ya zuwa na aikin soji.