Rumsfeld ka iya fuskantar tuhuma bisa ba da umarnin azabtarwa
November 11, 2006Wata kungiyar lauyoyi dake kare mutanen da aka tsare a sansanin sojin Amirka dake Guantanamo Bay a can kasar Cuba, sun ce zasu yi karar sakataren tsaron Amirka mai barin gado Donald Rumsfeld dangane da rawar da ya taka wajen ba da umarnin azabtar da jama´a. Kungiyar ta ce a ranar 14 ga wannan wata na nuwamba zata gabatar da karar na aikata laifi a wata kotu dake nan Jamus. Kungiyar zata bukaci masu shigar da kara na tarayyar Jamus su fara wani bincike wanda zai duba akan zargin da ake yiwa manyan jami´an Amirka bisa ba da umarnin aikata laifukan yaki a karkashin matakan nan na yaki da ta´adda. Tsohon mai bawa fadar White House shawara akan harkokin shari´a kuma atoni janar a yanzu Alberto Gonzales da tsohon darakatn hukumar leken asirin Amirka George Tenet da wasu mayan jami´an Amirka na daga cikin wadanda za´a yi kararsu.