1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rumsfeld a Iraki

Zainab A MohammedJuly 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6B

Sakataren tsaro na amurka Donald Rumsfeld ya kai ziyarar bazata a kasar Iraki ,domin ganawa da comandojin sojin Amurka da Jamian Irakin.Ya bayyana cewa zasu tattauna batun tsaro da sasanta kann kasar da horar da jamian tsaron Irakin,amma banda batun janye dakarun Amurkan daga wannan kasa.Wannan ziyara da Rumsfeld dai tazo ne adaidai,lokacinda mutane 7 suka rasa rayukansu a harin Bomb a gabashin birnin bagadaza a yau,.A halin da ake ciki a irakin kuma,prime minista Nouori al-Maliki ya bayyana cewa an gano wani shirin da sojin sakai sukayi na mamaye yankin gabashin kasar.