Rugujewar tattalin arzikin duniya | Zamantakewa | DW | 05.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rugujewar tattalin arzikin duniya

Masana na bayyana fargabar duniya za ta sake tsunduma cikin mummunar taɓarɓarewar tattalin arziki

default

Wani yaro da babansa kan juji

Sannu a hankali dai rikicin tattalin arziki yana yaɗuwa a duniya, kuma barazanar da hakan zai jawo sai ƙara bayyana yake yi. To shin wane irin hatsarine hakan yake ga makomar tattalin arzikin duniya? Ya ya girman barazanar yake idan aka sake tsunduma cikin wani sabon rikicin tattalin arziki, amasar waɗannan tambayoyi ne ke ƙumshe a rohoton namu.

To amsa waɗannan tambayoyi dai zamu iya farawa da kalaman da Thomas Straubhaar daraktan cibiyar tattalin arziki duniya da ke birnin Hamburg ya yi.

"Yace kamar dai marar lafiyane da ya fara samun sauƙi, kuma aka sallamo shi daga asibiti, za'a iya cewa ya samu lafiyane kawai, idan ya daina tafiya kan kujerar guragu"

Kafin a amsa waɗannan bayanan dai sai kuma an duba kalaman shugaban cibiyar tattalin arziki ta Kiel Dennis Snower, wanda yace hatsarin rugujewar tattalin ariki yana fiskatar ɗaukancin duniya, a faɗarsa harma da ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziki a duniya.

"Tana iya yuwa ƙasar Amirka ta faɗa cikin mummunar rugujewar tattalin arziki"

A ƙashin gaskiya dai akwai alamun tattalin arzikin duniya zai iya shiga yanayi na tangal tangal. Tsakanin watan Aprilu da Juni bana kaɗai, tashin farashin kaya ya kai kusan kashi biyu cikin ɗari. Rashin aikin yi a Amirka ya kai ƙololuwa, wato kusan kashi goma cikin ɗari. To sai dai idan Amirka ta shiga uku, to Turai dole su tagumi, kamar yadda Thomas Staubhaar yace.

"Abune mai yuwa, idan aka ce mutum hanya guda yake da ita, don haka na ke cewa alherine ga Turai idan Amirka ta sake tsayawa da ƙafafuwanta"

To sai dai wannan ya baiwa ƙasar China damar ci gaba da kankane al'amuran tattalin arziki na duniya, musamman a nahiyar Afirka. Inji masanin

"China tana sayan ma'adinan ƙarƙashin ƙasa masu yawa da kuma makamashi a duk inda ta ga halin yin hakan, ta haɓaka su, tana rage faracin su, tana kuma bunƙasa su yadda za ta iya, kai China ta kasance ƙasa mafi taka rawa a fannin kasuwannin ma'adinai na ƙasa da ƙasa"

A dai-dai lokacin da ƙasashen China da Indiya ke ƙara haɓaka, wata matsalar da ake gudu itace yadda za'a faɗa tashin hankali na siyasar da ta shafi ma'adinai inda ƙasashen da suka mallaki irin wannan arzikin za'a riga juya su. Yayin da harkar fitar da kayaki a kasuwannin duniya shi ma zai fiskanci gasa.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Danhong Zhang.

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal.