Rufe Taron kasa da kasa kan fasahar eLearning a Dakar. | Siyasa | DW | 30.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rufe Taron kasa da kasa kan fasahar eLearning a Dakar.

Fasahar zamani na ilimi ta na'ura mai kwakwalwa a Afirka

default

Ɗalibai na nazarin Komfuta

An kammala taron yini uku akan sabbin fasahun zamani na ilimi da sadarwa ta na'ura mai kwakwalwa ko kuma eLearning. Taron wanda ya gudana birnin Dakar ɗin ƙasar Senegal, ya samu halartan wakila daga sassa daba-daban na Duniya kimanin 1,300 waɗanda ke fatan cin moriyar wannan dama.

Manufofin maharta taron dai shine samun damar waɗannan sabbin fasahu na hanyoyin ilimin zamani da sadarwa ta na'ura mai aiki da kwakwalwa,tare da musayar yawu da kwararru dangane da yadda tsarin yake.

Kazalika bayan ƙasidu daga malamai da kwararru 300 daga wannan fage, wannan wata damace ta sabuwar fasaha daga sassa na Duniya da Afirka zata iya cin gajiyarsa. Kamar yadda wata masana'antar Amurka ta gabatar da wata na'ura mai kama da karamin llo da za a iya amfani dashi wajen harkokin koyarwa.

Eine Schauspielerin bei der Aufnahme von Radionovelas für die Bildungsreihe Learning by Ear

Wasan kwaikwayo ta Radiyo

A kokarin da Majalisar Ɗunkin Duniya keyi na cimma manufofinta na ilimantar da mafi yawan Al'umma,yaya wannan tsarin ilimantar na eLearning zai cimma nasara a ƙasashen Afirka musamman wadanda ke kudu da sahara. Abdoulaye Wade shine shugaban ƙasar Senegal kuma mai masaukin baƙin wannan muhimmin taro. Yace

"Muna muradin amfani da wannan fasaha ta sadarwa a harkokin iliminmu, musamman wa jami'an horarwa.Kamar yadda mukeyi a nan Senegal. Amma wannan tsari na eLearning muna amfani dashi ne kaɗai a jami'oi mu,amma ba makarantun dake kasa ba. Abun nufi anan a matakai na sama".

Tim Unwin dake zama shugaban sashin kula da inganta sadarwa na hukumar UNESCO kuma waɗanda suka shirya taron, yana da wani ra'ayin daban. Domin acewarsa wannan tsari ne daya kamata ayi shi a kowane mataki na ilimi, ba tare da la'akari da matakinsa ba...

Yace" a ganina abun da keda muhimmanci da tsarin ilimi na eLearning ba abunda ya kunsa ba ne. Amma yadda za a samu hadin kai wajen aiwatar dashi zuwa sassa daban-daban ,da kuma yadda za a tabbatar da nasara shi kansa tsarin da muhimmancinsa wajen raya cigaba. Tsarin eLearning na bukatar musayar ra'ayoyi tsakanin jama'a, ko al'umma dangane da tushen kowane abu da yadda zaa aiwatar dashi domin cimma nasara. Wannan taro ya tanadi muhimman abubuwa, da yadda za a aiwatar dasu domin cimma nasarar wannan tsari na ilimantarwa"

Aufnahme von Radionovelas für die Bildungsreihe Learning by Ear

Amfani da na'urar Komfuta

To shima joshua Mallet, kwararren masanin harkokin ilimi dake cibiyar kasa da kasa mai nazarilin ilimin wayar tafi da gidan ta salula kuma ɗan kasar Ghana, ya ce wannan tsari na ilimin fasaha baya bukatar wani matsayi ko matakin mutum...

" Wani yana samun dala ɗaya ne kachal a kowace rana,amma zaka ganshi da wayar salul.zai iya kasancewa wanda bai taɓa samun ilimin rubutu ko karatu ba amma ya mallaki wayar hannu. Na je ƙasa ta Ghana inda naga irin 'yammatan nan masu daukar kaya suna talla akansu a kasuwa,sai naga wata daga cikinsu dauke da wayar salula, dana tambaye ta sai tace min tana da masu cinikinta da suke magana ta waya. Ga gani wannan yarinya da bata yi karatu ba tana amfani da wayar salula wajen kasuwanci"

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Mohammed Nasir Awal