Rufe gidan yarin Guantanamo Bay bai taso ba ..
January 10, 2006Talla
Mahukuntan Amurka sun yi watsi da kiran da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar musu na bukatar rufe gidan yarin Guantanamo Bay dake kasar Cuba.
Tuni dai mahukuntan na Amurka suka mayar da martanin cewa, akwai alfanun barin gidan yarin na Guantanamo Bay.
Angela Merkel dai tayi wannan furucin ne kwanaki kadan kafin kai ziyara izuwa birnin Washinton , inda aka shirya cewa zasu yi ganawar ido da ido da shugaba Bush
Ya zuwa yanzu dai an kiyasta cewa akwai daurarru a kalla kusan dari biyar a cikin gidan yarin na Guantanamo Bay, wanda da yawan su na tsare ne ba tare da an yanke musu hukunci ba, koda yake Amurka tace basu da yanci irin na fursunoni, domin su makiya zaman lafiya ne.