Rudanin siyasa a kasar Haiti
June 14, 2016Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawan kasar suka kira magoya bayan su da yin kwanan zaune na nuna kishin kasa, a wani mataki na nuna kawo karshen mulkin shugaban rikon kwaryar kasar da wa'adin mulkin sa ya kawo karshe. Sai dai sanarwar ta gwamnatin ta Haiti da aka wallafa ta jim kadan kafin lokacin soma aikin dokar hana fitan, ta ce daukan wannan mataki dai ya biyo bayan samun wasu bayannai na sirri da ke cewa akwai yuyuwar yin amfani da wannan dama domin tadda zaune tsaye.
An dai haramta duk wata zirga-zirgar mutane, ko ta ababan hawa a dukannin titunan biranen kasar sai dai motocin 'yan sanda, da kuma na agajin gaggawa. Kasar ta Haiti dai ta tsunduma cikin wani yanayi na rikicin siyasa tun bayan da aka soke tsarin harkokin tafiyar ta zabukan kasar a watan Janairu da ya gabata.