1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rubzawar kasuwa a Moscou

A birnin Mosco na kasar Rasha ginin wata kasuwa ya rubza, inda ya hadasa mutuwar mutane kussan 40, da kuma jikkata wasu da dama.

Rahotani daga ƙasar, sun ambata cewar, mutanen da ke kwance, a assibitoci na cikin matsananci hali.

Gwamnati ta girka wani komiti domin gudanar da bincike a game da mussababin wannan haɗari.

Kamin komtin ke gabatar da sakamakon binciken, hasashe, na ɗora alhakin rubzawar ginin ga tulin dussa ƙanƙara, da ke kansa, wasu kuma na zargin cewar ginin tunda farko, ba a yi shi ba, bisa ƙa´ida.