1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rsaha ta janye daga yarjejeniyar CFE wadda ta ƙayyade aikin soji a Turai

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu kan wata doka wadda ta dakatar da biyayyar da kasar ke yiwa yarjejeniyar da aka ƙulla a lokacin yaƙin cacar baka don ƙayyade yawan dakaru a nahiyar Turai. Kamfanin dilancin labarun Rasha ya rawaito fadar Kremlin na ba da wannan sanarwa a yau juma´a. Yarjejeniyar da ake yiwa laƙabi da CFE ta ƙayyade yawan motocin yaƙi da sauran kayan soji da ake amfani da su a Turai don tabbatar da tsaron lafiyar wannan nahiya. A cikin watan yuni Putin ya ba da umarnin dakatar da aiki da yarjejeniyar saboda adawa da ya ke yi da shirin Amirka na kafa kandagarkin makaman nukiliya a gabashin Turai.